Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Laraba

1 Satumba 2021

13:29:20
1175549

MDD, Na Bukatar Yin Aiki Da Iran Domin Samar Da Zaman Lafiya Da Ci Gaba_Guteress

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guteress, ya bayyana bukatar yin aiki da Iran domin tabbatar zaman lafiya da tsaro da ci gaba mai daurewa a fadin duniya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : A wata wasika da ya aike wa shugaban kasar ta Iran, Ebrahim Ra’isi, babban sakataren na MDD, ya taya zababben shugaban kasar ta Iran murna akan zabin da akayi masa, tare da fatan yin aiki tare da sabuwar gwamnatin ta Iran.

Mista Guteress, ya kara da cewa, ‘’shugabancin ka, ya zo a daidai wani lokaci mai tsanani a fadin duniya, inda ake fama da annobar korona, canjin yanayi da rikice rikice da suka mamaye duniya ciki har da a yankin gabas ta tsakiya’’.

A don haka babban sakataren na MDD, ya bayyana fatansa ga shugaban kasar ta Iran, na yin aiki tare, domin cimma burin da aka sanya a gaba na tabbatar da zaman lafiya da tsaro, da ci gaba mai daurewa da kare hakkin dan adam a duniya baki daya.

342/