Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Laraba

1 Satumba 2021

13:17:06
1175539

​MDD Ta Bayyana Cewa A Shirye Take Ta Yi Aiki Da Kasar Iran A Bangarori Daban-Daban Na Al-Amuran Duniya

Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa MDD a shirye take ta yi aiki da jumhuriyar Musulunci ta Iran a wurare da dama wadanda suka shafi kasashen duniya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Guterres ya bayyana haka ne a wata wasikar da ya rubutawa sabon shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi, inda a cikinta ya taya shi murnar zabensa a matsayin shugaban kasar Iran. Sannan ya yi masa fatan alheri a shugabancinsa, musamman ganin ya kama aiki a dai dai lokacinda kasar Iran ta ke fama da matsaloli da daban-daban, daga cikin har da cutar covid 19 wacce take yaduwa a cikin kasar take kuma daukar rayukan wasu da dama. Har’ila yau ga kuma matsalolin kasashen gabas ta tsakiya da kuma sauyin yanayi a duniya.

Babban sakataren ya kammala da cewa arzikin kasar Iran wanda ya hada da na mutane masu hazaka da kuma na ma’adinai zasu taimaka wajen kawo ci gaba a kasar da kuma duniya gaba daya.

342/