Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Laraba

1 Satumba 2021

13:15:33
1175528

Iraki: An Kai Hari Kan Ayarin Motocin Daukar Kaya Na Sojojin Amurka A Lardin Addiwaniyya Na Kudancin Kasar

Kafafen yada labarai daga kasar Iraki sun bayyana cewa an kai hari kan ayarin motocin daukar kaya na kasar Amurka wadanda suke wucewa ta Lardin Addiwaniya daga kudancin kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Majiyar muryar Jumhuriyar Musulunci ta Iran (MJI) ta nakalto kamfanin dillancin labaran ‘Assabirun News’ na kasar Irakin ya na fadar haka a shafinsa na Instegram a safiyar yau Talata.

Labarin ya kara da cewa ba wanda ya dauki alhakin kaiwa tawagar motocin daukar kaya na sojojin Amurkan harin.

Har’ila yau a ranar Asabar da ta gabata ma, an kaiwa wata tawagar motocin daukar kananan makamai da kayakin bukatun sojojin kasar na Amurka a lokacinda suka shigo kasar daga kasar Kuwai.

Tun shekara ta 2003 Amurka da Burtaniya suka mamaye kasar Iraki, tare da zargin gwamnatin kasar da kera makamai kare dangi, wadanda ba’a samesu ba har yanzun.

A farkon shekarar da ta gabata ce majalisar dokokin kasar ta Iraki ta bukaci a kawo karshen samuwar sojojin kasashen waje a kasar, bayan kisan da gwamnatin Amurka ta yi wa Janar Kasim Sulaimani da kuma Mahdi Al-Muhandis a birnin Bagdaza a farkon shekarar.

342/