Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Laraba

1 Satumba 2021

13:14:37
1175527

​Amurka Ta Mayar Ayyukan Ofishin Jakadancinta A Afghanistan Zuwa Qatar

Gwamnatin kasar Amurka ta mayar da dukkanin ayyukan ofishin jakadancinta da ke birnin Kabul na kasar Afghanistan zuwa birnin Doha na kasar Qatar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Tashar Russia Today ta bayar da rohoton cewa, sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ya sanar a daren jiya cewa, ya zuwa yanzu gwamnatin kasar Amurka ta mayar da dukkanin ayyukan ofishin jakadancinta da ke birnin Kabul na kasar Afghanistan zuwa birnin Doha na kasar Qatar, inda za ta ci gaba da gudanar da ayyuka da suka shafi Afghaistan daga can.

Ya ce za su ci gaba da kokarin ganin sun taimaka ma sauran Amurkawan da suka rage a kasar Afghanistan a halin yanzu wadanda yawansu zai kimanin mutane 100, matukar dai suna bukatar barin kasar.

Blinken ya bayyana hakan ne bayan tashin jirgi na karshe da ke dauke da sojojin Amurka da suka mamaye kasar Afghanistan tsawon kimanin shekaru 20 da suka gabata.

Yanzu haka dai wannan mataki da shugaban Amurka Joe Biden ya dauka na fitar sojojin Amurka ba zata daga Afghanistan, yana ci gaban da shan suka daga bangarori daban-daban na ‘yan siyasar Amurka, da suka hada har da ‘yan jam’iyyarsa ta Democrat.

Baya ga haka kuma wasu daga cikin manyan janar-janar a ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon, sun bayyana matakin na Biden da cewa shi ne ya jefa kasar Afghanistan a cikin halin da shiga a yanzu, tare da kuma bayyana hakan a matsayin babban abin kunya ga Amurka.

342/