Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban Biden na kasar Amurka ya na fadar haka a lokacinda yake ganawa da sabon Firai ministan haramtacciyar kasar Isar’ila (HKI) Naftali Bennett a washingtong a jiya Asabar.
Jami’in ya kara da cewa zabin diblomasiyya a wajen Biden shi ne ‘tattaunawar Vienna a kasar Austria’ dangane da komawar Amurka cikin yarjejeniyar JCPOA, sannan wasu zabin kuma ya na nufin yaki ne, idan tattaunawar Vienna ta kasa tilastawa Iran amincewa da bukatunta.
Iran dai ta bayyana cewa ba za ta amince da komawa kan yarjejeniyar JCPOA ba, sai idan Amurka ta dauke dukkan takunkuman da gwamnatin Trump ta dorawa kasar bayan ya fitarda kasar daga yarjejeniyar ta JCPOA a shekara 2018.
342/