Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Litinin

30 Agusta 2021

12:49:34
1174853

Biden: Akwai Yiwuwar A Sake Kai Wani Harin Ta’addanci A Kabul

Amurka ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar sake kai wani harin ta’addanci makamancin wanda aka kai a filin jirgin saman Kabul nan da ‘yan sa’o’i.

ABNA24 : Gidan rediyon Faransa bayan samun wasu bayanai daga tawagarsa ta tsaron kasa, shugaba Joe Biden ya fada a wata sanarwa cewa za a ci gaba da kai harin jirgi mara matuki a kan kungiyar Khorasan ta IS da ta dauki alhakin mummunan harin Kabul.

Biden ya ce yanayin da ake ciki a halin yanzu yana da matukar hadari, kuma har yanzu akwai barazanar hare haren ta’addanci a filin tashi da saukar jiragen sama na Kabul, yana mai cewa kwamandojinsa sun shaida masa yiwuwar hakan.

Fiyeda mutane dubu 112 ne suka tsere daga Afghanistan ta wurin shirin kwashe mutane dac Amurka ke jagoranta tun da Taliban ta kwace mulkin kasar makonni 2 da suka wuce.

Fiye da mutane 100 suka mutu a harin da IS ta kai yayin kwashe mutane a filin jirgin saman Kabul, ciki har da dakarun Amurka 13.

342/