Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Asabar

28 Agusta 2021

11:20:59
1174175

Amurka Ta Hallaka Wani Babban Mamba Na Kungiyar IS A Afghanistan

Rundinar sojin Amurka ta sanar da kashe wani jigon kungiyar IS, a kasar Afghanistan.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Wata sanarwa da rundinar ta fitar, ta ce an kai wani harin jirgi marar matuki, wanda a yayinsa aka kashe wani babban mamba na kungiyar IS- a yankin Kohrasan, wanda shi ne ya sanar da daukar alhakin kai harin filin jirgin saman Kabul.

Harin dai shi ne irinsa na farko, a hukumance da Amurka ta kai tun bayan harin na ranar Alhamis, wanda a yayinsa sojojin Amurka 13 da fararen hula kimanin 90 suka mutu.

Dama dai kafin hakan Shugaban Amurka Joe Biden ya sha alwashin farautar wadanda suka kai harin na Kabul, yana mai cewa za su dandana kudarsu.

An dai bayyana harin da mafi muni ga sojojin Amurka a Afghanistan, tun bayan na shekarar 2011.

342/