Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Asabar

28 Agusta 2021

11:16:45
1174171

​Biden: Za Mu Mayar Da Martani Kan Daesh Dangane Da Harin Kabul

Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya yi barazanar mayar da mummunan martani a kan kungiyar Daesh, bayan harin da kungiyar ta kai a filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Kabul a kasar Afghanistan.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Tashar almayadeen ta bayar da rahoton cewa, a cikin jawabinsa da ya gabatar a jiya dangane da harin da kungiyar daesh ta kaddamar a fikin sauka da tashin jiragen sama na birnin Kabul, Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya bayyana cewa, Daesh za ta dandana kudarta kan wannan hari.

Dangane da halin da ake ciki a kasar ta Afghanistan, da kuma aikin kwashe sojojin Amurka da sauran ‘yan kasar wadanda suka yi aiki tare da sojojin Amurka, Joe Biden ya ce za su kammala aikin kwashe sojojinsu da sauran Amurka gami da wasu daga cikin wadanda suka yi aiki tare das u daga nan zuwa ranar 31 ga watan Agusta.

Ya ce rahotanni na asiri sun tabbatar musu da cewa Daesh c eta kai wannan hari a filin sauka da tashin jiragen sama na Kabul wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin Amurka 13 da kuma jikkatar wasu, gami da mutuwar fararen hula da dama, kuam a cewarsa Amurka za ta mayar da mummunan martani kan hakan a kan kungiyar Daesh.

Rahotanni sun tabbatar da cewa mutane fiye da 170 ne dai suka rasa rasa rayukansu a harin na birnin Kabul, da suka hada da sojojin Amurka 13 da kuma ‘yan Taliban 30.

342/