Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Alhamis

26 Agusta 2021

10:55:26
1173404

​Kasar Venuzuwela Ta Bukaci Kotun ICC Ya Sanar Da Takunkumin Amurka Kan Kasashen Latin Amurka A Matsayin Cin Zarafin Bil Adama

Mataimakiyar shugaban kasar Venuzuwela Delcy Rodriguez da ta ke bayani ga manema labarai a birnin Karakas fadar mulkin kasar ta bayyana irin yadda takunkumin da kasar Amurka ta kakabawa kasarta ya take hakkin Alummar kasar a bangaren lafiya da ci gaban tattalin arziki, don haka ta bukaci babban kotun duniya mai hukunta manyan laifuka ta ICC da ta sanar da Takunkumin na Amurka a matsayin cin zarafin bil Adama,

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Amurka ta kakabawa kasar takunkumin karya tattalin arziki daban daban domin durkusar da gwamnatin Nicola Madoro tare da maye gurbinsa da shugaban Yan adawa na kasar Juan Guido, takunkumin ya kun shi kwace kadarorin kasar da ke kasashen waje ba bisa ka’ida ba, da kuma toshe tattalin Arzikin kasar da hakan ya jefa miliyoyin mutanen kasar cikin mawuyacin hali.

A watan Fabarerun shekara ta 2020 gwamnatin kasar ta kai karan Amurka gaban kotun ICC in da ta bayyana matakin da Amurka ta ke dauka a kanta a matsayin cin zarfafin dan Adam, Wakilan gwamnatin Kasar da na ‘Yan adawa suna tattaunawa a kasar Meziko domin gano hanyoyin warware matsalar tattalin arziki da siyasa da kasar ke ciki.

342/