Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Parstoday
Talata

24 Agusta 2021

11:47:23
1172715

Afganistan:Taliban Ta Ce Ba Za Ta Karawa Amurka Wa’adin Fita Daga Kasar Ba

Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya na cikin tsaka mai wuya, bayan da kungiyar Taliban ta ce ba za ta kara wa’adin da ta bawa Amurka na ta kwace sojojinta da duk abinda ta mallaka ta bar kasar ba.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : ya bayyana cewa ma su bawa shugaban kasar ta Amurka shawara kan al-amuran tsaro sun bukace shi ya tsaida shawara daga yau Talata na yiyuwar a kwace dukkan sojojin Amurka fiye da 5000 da suke cikin kasar Afganistan haryanzun da kuma rashin yiyuwar hakan.

A halin yanzu dai sojojin Amurka 5,800 ne suke jiran a fitar da su daga kasar Afganistan nan da ranar 31 ga watan Augusta da muke ciki, wanda kuma shi ne wa’adin da kungiyar Taliban ta bawa Amurka na ta kwace ye nata-Ye nata ta bar kasar.

Wasu majiyoyin tsaro na kasashen yamma suna gargadi kan yiyuwar a kaiwa sojojin Amurka harin ta’addanci a kasar Afaganistan.

342/