Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Litinin

23 Agusta 2021

12:03:52
1172353

​Nikki Haley: Ta Zargi gwamnatin Joe Biden Da Mika Kai Ga Kungiyar Taliban

Tsohuwar jakadiyar Amurka a MDD Nikki Haley ta soki shugaban Amurka Joe Biden kan yadda ya mika kai ga kungiyar Taliban har ta kwace kasar Afganistan.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Nikki Haley ta bayyana haka ne a hiran da ta hadata da tashar CBS ta kasar Amurka a jiya Lahadi.

Ta kuma kara da cewa abinda shugaban Biden yayin shi ne mika kai gaba daya ga kungiyar Taliban, inda ya mika mata sansanin sojojin sama na Bagram tare da dimbin makamai na biliyoyin dalar Amurka da suke cikinsa.

Banda haka Haley ta kara da cewa Biden yayi kuskure da ya janye sojojin Amurka daga Afganistan, tun kafin ya kwace Amurkawa da kawayenta da suke cikin kasar.

Daga karshe Nikki Haley ta kammala da cewa shugaba Biden ya yi kurakurai da dama a shirinsa na janyewa daga kasar Afganistan.

342/