Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Jummaʼa

20 Agusta 2021

15:20:41
1171401

Guterres: MDD A Shirye Take Ta Tattauna Da Taliban Matuƙar Za Ta Amince Da Wasu Sharuɗɗa

Babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana cewar majalisar za ta yi amfani da buƙatar ƙungiyar Taliban na neman a amince da ita a hukumance wajen matsa mata lambar ta amince da kafa gwamnatin haɗaka a ƙasar da kuma kare haƙƙoƙin bil’adama musamman ma mata.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Mr. Guterres ya bayyana hakan ne a zaman da aka gudanar a MDD in da ya ce shi kansa a shirye ya ke ya zauna teburin tattaunawa da Taliban amma da sharaɗin kan me za a tattauana sannan kuma da waye za a tattaunawar yana mai cewa jami’an Majalisar da suke birnin Kabul suna da alaƙa da ƙungiyar ta Taliban.

Babban sakataren MDD ya ce wajibi ne ‘yan ƙungiyar Taliban ɗin su amince da kafa gwamnatin haɗaka da za ta ƙunshi dukkanin ɓangarori na al’ummar Afghanistan kamar yadda kuma ya ce wajibi ne su tabbatar da cewa za su kare haƙƙoƙin al’ummar ƙasar musamman ma mata.

Tun dai bayan da ta ƙwace madafa iko a ƙasar ta Afghanistan ƙungiyar ta Taliban ta sanar da aniyarta na samar da sauyi cikin yanayin mu’amalarta da al’ummar ƙasar musamman mata, lamarin da da dama suka yi na’am da shi duk kuwa da yadda wasu suke ɗarɗar da wannan alƙawari da ‘yan ƙungiyar suka yi.

342/