Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Talata

17 Agusta 2021

14:41:00
1170610

Haiti : Adadin Wadanda Suka Mutu A Girgizar Kasa Ya Karu Zuwa 1,419

Adadin wadanda suka mutu sanadiyyar girgizar kasa mai karfi da ta auku ranar Asabar a kudu maso yammacin Haiti, ya karu zuwa 1,419.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA : Hukumar kare al’umma ta kasar, ta ce girgizar mai karfin maki 7.2 ta kuma jikkata a kalla mutane 6,900 yayin da ta lalata gidaje sama da 37,000.

Hukumar ta bayyana a dandalin twitter cewa, ta na amfani da jirgi mai saukar ungulu wajen ci gaba da kwashe wadanda suke cikin yanayi mai tsanani daga yankin, ta yadda za su samu kulawar da ta dace.

342/