Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Talata

17 Agusta 2021

14:37:02
1170606

Yawan Mutanen Da Suka Rasa Rayukansu Sanadiyyar Girgizar Kasa A Haiti Ya Kai Mutane 1,297

Yawan wadanda suka rasa rayukansu a girgizar kasa mai karfin ma’aunin Richter 7.2 wacce ta aukawa kasar Haiti a ranar Asabar da ta gabata ya kai mutane 1,297 kuma har yanzun ma’aikatan ceto suna aiki tukuru a wasu yanku a kasar don neman wadanda suke da suaran shan ruwa ko kuma zakulo gawakin wadanda suka mutu.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA : Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewa a halin yanzu asbitocin kasar a cike suke da wadanda suka ji rauni sanadiyyar girgizar kasar, wanda yawansu ya kai 5,700.

Tuni dai gwamnatin kasar Ta Haiti ta bukaci taimako daga kasashen duniya, don jinyan wadanda suka ji rauni. Labarin ya kara da cewa a arewa maso yammacin garin Jeremia likitoci suna jinyar wadanda suka ji rauni karkashin itatuwa, ko a kan tatifa a kasa saboda cikar asbitocin kasar.

342/