Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Litinin

16 Agusta 2021

15:18:36
1170244

​Duniya Na Ci gaba Da Maida Martani Bayan Da Taliban Ta Kwaci Mulki

Kasashen duniya na ci gaba da maida martani bayan da kungiyar Taliban ta kwace mulki a kasar.

ABNA24 : Yayin da Joe Biden ya fara shan suka kan halin da kasar ta shiga, shugaban ya ce ‘’kara shekara guda ko biyar ba zai sauya wani abu ba idan har sojojin Afganistan sun kasa ko kuma sun ki tabaka komai wajen kare kasarsu’’.

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump, ya bukaci Biden da ya yi murabus saboda kasawa a Afganistan.

A nata bangare Rasha ta ce jakadanta a Afganistan zai gana da jagoran harkokin tsaro na kungiyar ta Taliban a ranar Talata.

China kuwa ta ce a shirye ta ke ta kula dangantaka ta amintaka da ‘yan Taliban.

Ita kuwa faransa ta ce batun kwashe ‘yan kasarta A Afganistan shi ne ta sanya a gaba.

Jamhuriyar musulinci ta Iran ta ce a shirye ta ke ta ciga da kokarinta na samar da zaman lafiya a kasar ta Afganistan, kamar yadda ministan harkokin wajen kasar Muhamad Jawwad Zarif ya bayyana.

342/