Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Lahadi

15 Agusta 2021

12:48:36
1169852

Hiati : Adadin Mutanen Da Suka Mutu A Girgizar Kasa, Ya Haura 300

Rahotanni daga Haiti na cewa akalla mutane 304 ne suka rasa rayukasnu sanadin wata mummunar girgiza kasa data aukawa kasar a jiya.

ABNA24 : Ko baya ga hakan da akwai mutane 1,800 da suka jikkata, a cewar hukumar kula da agajin gaggawa ta kasar.

Bayanai sun ce an fuskanci girgiza mai karfin maki 7.2 a ma’aunin girgizar kasa.

Girgizar kasar ta lalata gidaje makarantu da wuraren ibada da dai saurensu.

Ana da fargabar adadin muaten da girgizar kasar ta shafa ya wuce hakan.

Tuni dai gwamnatin kasar ta ayyana dokar ta baci ta tsawon wata guda biyo bayan aukuwar lamarin.

Fira ministan kasar Ariel Henry, ya bukaci jama’ar kasar da kada su tsorata su kuma taimakawa junansu a wannan hali da ake ciki.

342/