Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Alhamis

12 Agusta 2021

13:33:12
1169086

Kamfanin Shell Zai Biya Diyyar Dalar Amurka Miliyon 111 Ga Mutanen Yankin Ogoni

Kamfanin haka da sarrafa danyen man fetur Shell a Najeriya zai biya diyyar dalar Amurka miliyan 111 ko naira Biliyan 45.9 don kawo karshen shari’ar da yake da mutanen yankin Ogoni daga kudancin Najeriya saboda gurmata yanayin da ta yi a yankin tun fiye da shekaru 50 da suka gabata.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Reuters ya nakalto kakakon kamfanin na Shell yana fadar haka a jiya Laraba

Labarin ya kara da cewa kamfanin zai biya mutanen Ejama-Ebubu na yankin Ogoniland dukkan wadannan kudade don kawo karshen shari’ar da ake da su kan gurbata yankinsu da danyen man fetur tun lolacin yayin babasar kasar tsakaninn shekara 1967-1970.

Mutanen yankin dai suna neman shell ta baya naira biliyon 180 a matsayin diyya kan wannan barnan, amma daga karshe aka daidaita kan naira biliyon 45.9.

Gurbacewar kasar yankin da danyen man fetur ya hana su samun ruwan sha mai tsabta, noma da kuma kama kifi shekaru fiye da 60.

342/