Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Talata

10 Agusta 2021

11:12:39
1168363

Amurka Ta Kakabawa Kungiyoyin Gwagwarmaya Na Kasashen Iraki Siriya Da Lebanon Takunkumi

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bada sanarwan dorawa kungiyoyi masu gwagwarmaya da ‘yan ta’adda wadanda take goyawa bayan a kasashen Iraki, Siriya da Lebanon sabbin takunkuman tattalin arziki.

ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, daukar wannan matakin ya nuna irin fushin da gwamnatin kasar Amurka take yi da wadannan kungiyoyi wadanda suka lalata shirin Amurka wargaza wadannan kasashe tare da amfani da kungiyoyin ‘yan yan ta’adda wadanda ta kirkiro don cimma wannan manufar.

A wani bayani wanda sashen tsaro na kasa da kasa a ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar a jiya Litinin, ya bayyana cewa sabbin takunkuman sun shafi kungiyoyi masu gwagwarmaya na Asa’ib Ahl al-Haq da Kata’ib Hezbollah na kasar Iraki, karkashin karkashin babban kungiyarsu ta Hashdushaabi ko (PMU), da kuma kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon, wacce take dangantawa da kasar Iran.

Bayanin ya kara da cewa takunkuman da aka dorawa wadannan kungiyoyi sun hada da basu makamai da dukkan abinda zai basu karfin yakar makiyansu.

Har’ila yau takunkuman sun shafi wasu ‘yan kasuwa a kasar Siriya wadanda suka hada Wael Issa da kuma Ayman Ashabbag banda haka takunkuman sun shafi wasu kamfanonin kasar Rasha guda uku a kasar ta siriya.

Ana saran gwamnatin kasar Amurka za ta buga cikekken bayanan wadannan sabbin takunkuman a cikin wata jaridar kasar nan gaba.

342/