Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Asabar

7 Agusta 2021

15:30:47
1167353

Iyalan Waɗanda Suka Mutu A Harin 9/11 Sun Buƙaci Biden Da Kada Ya Zo Wajen Bikin Tunawa Da Harin

Iyalan mutanen da harin 11 ga watan Satumba da aka kai Amurka ya ritsa da su sun buƙaci shugaban Amurkan Joe Biden da kada ya halarci bikin tunawa da harin na bana matuƙar dai bai cika alƙawarinsa na fitar da takardun sirri da suke bayanin hannun da gwamnatin Saudiyya take da shi cikin harin.

ABNA24 : A wata wasiƙa da ƙungiyar iyalan waɗanda harin 11 ga Satumban ya ritsa da su suka fitar a jiya Juma’a, iyalan sun tunatar wa shugaba Biden ɗin kan alƙawarin da yayi yayin yaƙin neman zaɓe na fitar da bayanan sirri na gwamnati da suke magana kan harin na 11 ga watan Satumba.

Don haka a cikin wasiƙar wanda kusan mutane 1800 suka sanya wa hannu, iyalan sun ce matuƙar shugaban Amurkan bai fitar da waɗannan takardun waɗanda a cikinsu aka yi bayanin rawar da gwamnatin Saudiyya ta taka yayin harin, to kada ya halarci taron tunawa da zagayowar shekarar harin da za a gudanar a biranen New York, Shanksville, Pennysylvania da kuma Ma’aikatar tsaron Amurka, wato Pentagon.

Iyalan waɗanda aka ritsa da su a harin na 9/11 sun jima suna buƙatar gwamnatocin Amurkan da suka gabata na su fitar da waɗannan takardun da suka yi bayanin hannun da gwamnatin Saudiyya ta ke da shi cikin wannan harin ta’addancin, amma dai suka yi kunnen uwar shegu da hakan.

Fadar White House ta Amurkan dai ta ce tana ci gaba da aiki tare da iyalan mutanen wajen ganin an biya musu wannan buƙata ta su.

An jima dai ana zargin gwamnatin Saudiyya da hannu cikin harin ta’addancin na 9/11 musamman ma bisa la’akari da cewa mafi yawa daga cikin ‘yan ta’addan da suka kai harin ‘yan asalin ƙasar Saudiyya ɗin ne.

342/