Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Alhamis

5 Agusta 2021

11:50:43
1166827

MDD Ta Damu Da Karuwar Ayyukan Ta'addanci A Nahiyar Afirka

Majalisar Dinkin Duniya, ta nuna matukar damuwarta game da karuwar ayyukan ta’addanci a nahiyar Afirka.

Da yake sanar da hakan sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya ce ayyukan masu ikirarin jihadi na ci gaba da zama gagarumar barazana ga zaman lafiya a duniya.

Mista Guterres, ya ce hakan na kara fitowa fili ne ta la'akari da yadda kungiyoyin ke yada rassa a wasu kasashen Afirka da nufin kafa kungiyoyi da suka ayyana a baya a kasashe irin su Siriya da Iraki.

Rahoton Guteres da aka mika wa kwamitin tsaro na MDD ranar Talata, ya ce kungiyar IS da wasu na ta'addanci na amfani da tsaikon da annobar Korona ta kawo wajen yada manufofinsu musamman ta Intanet.

Kasashen da Majalisar Dinkin Duniyar ta ambato a matsayin wuraren da da kungiyoyin ta’addancin ke kafa rassansu a nahiyar ta Afirka, su ne Mali da Burkina Faso da Chadi da Kamaru da Najeriya da Nijar sai kuma Muzambik da kuma kasar Tanzaniya.

342/