Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Talata

3 Agusta 2021

13:22:29
1166154

​Afganistan : Shugaba Ghani Ya Dora Alhakin Tabarbarewar Al’amuran Kasarsa Ga Amurka

Shugaba Ashraf Ghani, na Afganistan, ya dora alhakin tabarbarewar al’amuran tsaron kasarsa ga matakin Amurka na janye gabadayan dakarunta ba tare da wani shiri ba daga Afgasnitan.

ABNA24 : Kalamman na Mista Ghani, na zuwa ne a daidai lokacin da mayakan Taliban ke matsa kaimi kan wasu manyan biranen kasar, a daidai lokacin da kuma sojojin na Afganistan ke kara azama wajen kwato yankunan dake hannun Taliban.

Rikici ya ta’azzara a kasar ne a farkon watan Mayu, lokacin da kungiyar Taliban ta kaddamar da munanan hare hare yayin da sojojin kasashen waje dake karkashin jagorancin Amukra ke kokarin kammala ficewa daga kasar.

A karshen watan Agusta nan ne Amurka ta ce za a karkare janye dakarunta daga kasar ta Afghanistan.

Shugaba Joe Biden na Amurka dai, ya bayyana ranar 11 ga watan Satumban 2021 din nan a matsayin ranar janye ragowar dakarun kasar daga Afghanistan bayan shafe shekaru 20 suna gwabza yaki da mayakan Taliban da na Al’Qaeda.

342/