Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Asabar

31 Yuli 2021

14:57:05
1165163

Kwamitin Tsaro MDD, Ya Tsawaita Takunkumin Shigar Da Makamai A Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya

Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya, ya amince da gagarimin rinjaye da kudirin tsawaita wa’adin takunkumin shigar da makamai a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da shekara guda.

ABNA24 : Kasashe 14 ne mambobin kwamitin suka amince da kudirin, sai kasar China wacce ta ce ba ruwan ta.

Jakadan Faransa, a MDD, Nicolas de Rivière, ya bayyana cewa wannan matakin yana da matukar mahimmaci saboda yadda al’amurra ke kara dagulewa a jamhuriyar Afirka ta tsakiyar.

Shi kuwa jakadan China a MDD, Dai Bing, ya bayyana matakin da cewa babban nakaso ne ga gwamnatin CRA, na tabbatar da zaman lafiya da hadin kan kasa.

Saidai A karon farko, cikin sassauci guda tara da kwamitin ya yi, ya amince da mika wa gwamnatin Afirka ta tsakiyar harsashai, matakin da kasashen Rasha da Kenya sukayi maraba da shi.

A watan Disamba na shekarar 2013 ne kwamitin tsaron MDD, ya kakaba takunkumin shigar da makamai kan kasar ta CRA, lokacin da ‘yan tawayen Seleka suka tumbuke shugaban kasar na lokacin François Bozize.

Kuma tun shekarar 2014 ne kasar ke karkashin kulawar dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD.

342/