Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Asabar

31 Yuli 2021

14:52:55
1165159

Amurka: An Bankado Cewa Trump Ya Bukaci Ma’aikatar Shari’a Da Ta Soke Sakamakon Zabe

Wasu bayanai na sirri da aka samu sun tabbatar da cewa, tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bukaci ma’aikatar Shari’a ta kasar da ta soke sakamakon zaben kasar a cikin watan Disamba.

ABNA24 : A zaman da kwamitin sanya ido da kuma gyare-gyare na majalisar wakilai ya gudanar, ya gabatar da bayanin cewa, an samu cikakkun dalilai da ke tabbatar da cewa, Trump ya matsa lamba kan ma’aikatar shari’a domin ta soke sakamakon zaben da aka bayyana cewa Joe Biden ne ya lashe shi.

Kwamitin ya gabatar da tabbatattun dalilai, wadanda suka ginu a kan shedu da kuma sautin dukkanin wayoyin da Trump ya yi da manyan jami’an ma’aikatar shari’a a na lokacin.

Haka nnan kuma kwamitin ya sha alwashin bin kadun wannan lamari da ya bayyana shi da cewa yana da matukar hadari ga makomar kasa.

Tun bayan da Trump ya sha kayi a zaben 2020, har aynzu bai yadda cewa ya fadia zaben ba, inda yake ikirarin cewa shi ne ya lashe zaben.

342/