Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Laraba

28 Yuli 2021

14:56:52
1164188

An Bukaci Mutane Su Ci Gaba Da Sanya Takunkumin Baki Don Dakile Yaduwar Covid-19

Cibiyar kula da cututtuka masu yaduwa ta kasar Amurka, a jiya Talata ta bada sanarwan cewa hatta mutanen da suka yi alluran riga kafin cutar Covid 19 dole ne su sanya mask ko takunkumin rufe baki don kare kansu ko kuma hana yaduwar cutar sabuwar nau’in cutar wacce ake kira Delta tana da tsanani.

ABNA24 : Tashar talabijin ta CNN ta bayyana cewa wannan labarin ya maida murna ciki ga Amurkawa da dama wadanda suke fatan za’a kawo karshen cutar ta Covid 19 a karshen wannan shekara.

Labarin ya kara da cewa, kimani watanni biyu da suka gabata ne CDC ta bayyana cewa ba dole ba ne Amurkawa wadanda suka yi alluran riga kafin cutar su sanya takunkuman rufe baki ba a cikin gida, sai gashi a jiya ta na cewa ko wadanda suka yi alluran yakamata su sanya takunkumin, musamman a inda cutar tafi yaduwa.

A halin yanzu dai gwamnatin shugaba Biden ta na nazarin yiyuwan tilastawa ma’aikatan gwamnati kasar yin alluran riga kafin, sanadiyar kara yaduwar cutar a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata.

342/