Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Talata

27 Yuli 2021

15:29:03
1163873

An Kama Shugaban Masu Tsaron Tsohon Shugaban Haiti, A Ci Gaba Da Binciken Kisan Gillan Da Aka Masa

Rundunar ‘yan sandan ƙasar Haiti sun sanar da kama shugaban masu tsaron tsohon shugaban ƙasar da aka kashe, Jovenel Moise a ci gaba da binciken da suke gudanarwa kan kisan gillan da aka yi wa tsohon shugaban a ranar 7 ga watan Yulin nan.

ABNA24 : Kakakin rundunar ‘yan sandan Marie Michelle ce ta sanar da hakan a wata tattaunawa da ta yi da kamfanin dillancin labaran AFP inda ta ce a jiya Litinin ne aka ‘yan sandan suka kama Jean Laguel Civil, shugaban masu tsaron tsohon shugaba Moise ɗin a ci gaba da binciken da ake yi kan kisan gillan da aka masa. Ana zargin Jean Laguel Civil da hannu cikin kisan gillan da aka yi wa tsohon shugaban a tsakar dare a gidansa lokacin da wasu mahara suka shigo gidan ba tare da sun fuskanci wata turjiya daga masu tsaron shugaban ba har suka shiga suka buɗe masa wuta. Rahotanni dai sun ce ana tsare da Mr. Civil ne a gidan yarin Delmas da ke kusa da babban birnin ƙasar Haitin, Port-au-Prince. Mr. Civil dai ya musanta zargin da ake masa yana cewa akwai siyasa cikin lamarin. A baya dai ‘yan sandan sun kama wasu mutane da dama cikin kuwa har da wasu ‘yan ƙasar Kolombiya da ake zargi suna da hannu cikin wannan ɗanyen aikin.

342/