Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Alhamis

22 Yuli 2021

13:41:38
1162347

Pfizer/BioNTech Zai Fara Sarrafa Rigakafin Korona A Afrika Ta Kudu

Hadin Guiwar Kamfanonin harhada magunguna na Pfizer/BioNTech, ya sanar da cewa zai fara sarrafa maganinsa na riga kafin korona a Afrika ta Kudu, daga shekara mai zuwa.

ABNA24 : Kamfanin ya ce zai yi hadin guiwa ne da cibiyar samar da riga kafi ta Biovac A Afrika ta Kudun, inda kuma yake fatan sarrafa rigakafin korona miliyan 100 a cikin shekara.

Wannan dai a cewar kamfanin zai baiwa nahiyar ta Afrika damar ta dogara da kanta wajen sarrafa rigakafin na korona.

An bayyana cewa wannan shi ne karon farko da za’a fara sarrafa rigakafi nau’in ARN messager, a Afrika, saidia dukkan ababen harhada maganin za’a kawo su ne daga turai.

Dama dai kafin kamfanin na Pfizer/BioNTech, shi ma kamfanin Johnson&Johnson wanda ke kawance da Aspen, ya bayyana shirinsa na sarrafa rigakafin na korona a Afrika.

Shugaba Cyril Ramaphosa, na Afrika ta Kudu, ya bayyana hakan da babban ci gaba, wanda zai bada damar samun daidaito wajen samun rigakafi ga kowa da kowa.

Hakan na zuwa ne biyo bayan cece-kucen da ake yi kan rashin adalci wajen samar da riga-kafin annobar, inda kasashe matalauta da masu tasowa suka dogara kan kasashe masu karfin tattalin arziki wajen yi wa al'ummarsu riga-kafin.

342/