Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Talata

13 Yuli 2021

17:54:24
1160261

Amurka Ce Ta Ingiza Masu Bore A Cuba, Inji Shugaba Diaz-Canel

Shugaban kasar Cuba, Diaz-Canel, ya zargi Amurka da shirya zanga zangar data barke a fadin kasarsa.

ABNA24 : Shugaba Diaz-Canel, ya ce matsin lambar Amurka kan tattalin arzikin kasar, shi ne ummul aba’isin boren da ya barke a tsibirin kasar.

Ya kuma sha alwashin tunkarar lamarin da kuma shawo kan matsalar.

Tuni dai gwamnatin Harare ta katse intanet a tsibirin dake fama da zanga zangar, da ta ce Amurka ta tsara.

Gwamnatin Cuba ta ce an dauki tsawon watanni ana tsara zanga-zangar gama garin.

Ministan harkokin wajen kasar Bruno Rodriguez ya ce Amurka ta ware miliyoyin daloli domin daukar nauyin kungiyoyin adawa.

Amurka dai ta yi watsi da zargin, tare da gargadin mahukuntan Harare kan murkushe masu zanga zangar.

Dubban mutane ne suka fantsama kan titunan da ke fadin Cuba domin neman dimokradiyya a tsibirin da ke karkashin mulkin kwaminisanci da karin alluran rigakafin korona.

342/