Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Lahadi

11 Yuli 2021

12:50:51
1159171

Amurka Ta Roƙi Кungiyoyin Gwagwarmayar Iraƙi Da Su Daina Kai Wa Sojojinta Hari

Wani babban jami’in Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ya roƙi ƙungiyoyin gwagwarmayar ƙasar Iraƙi da ‘su dakatar’ da hare-haren da suke kai wa sojojin Amurkan da suke ƙasar Iraƙin.

ABNA24 : Muƙaddashin mataimakin sakataren harkokin wajen Amurkan Joey Hood ne yayi wannan kiran a wata hira da yayi da tashar talabijin ɗin nan ta Al-Arabiyya malakar ƙasar Saudiyya inda ya ce, ya fahimci cewa wasu daga cikin waɗannan ƙungiyoyi masu ɗauke da makami ba su yarda da Amurka take ƙoƙarin yi a Iraƙin na faɗa da ‘yan ƙungiyar ISIS ba, don haka sai ya ce: muna kiransu sannan muna roƙonsu da su bar haka nan”.

Hood yayi ikirarin cewa Amurka ba tana yaƙi ne kai tsaye da ƙungiyoyin gwagwarmayar na Iraƙin ba ne, don haka ya ce ci gaba da kai musu hari ba zai amfani kowa ba.

Wannan roƙo na Amurkan yana zuwa ne sakamakon wasu gungun hare-hare da ƙungiyoyin gwagwarmayar Iraƙi suka ƙaddamar kan sojoji da sansanonin Amurka a ci gaba da ƙoƙarin da suke na tilasta wa Amurka barin ƙasar.

Hare-haren na ƙungiyoyin gwagwarmayar suna zuwa ne a matsayin mayar da martani ga wani hari da sojojin Amurkan suka kai kan wani sansanin dakarun sa kai na Iraƙin da ake kira da Hash al-Sha’abi a kan iyakan ƙasar Iraƙin da Siriya da yayi sanadiyyar shahadar huɗu daga cikin na gwagwarmaya.

Ma’aikatar tsaron Amurkan dai ta ce an kai harin ne bisa umurnin shugaban Amurkan Joe Biden, lamarin da ‘yan gwagwarmayar suka sha alwashin ɗaukar fansa.

342/