Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Jummaʼa

9 Yuli 2021

13:53:51
1158481

‘Yan Sandan Haiti Sun Kashe Mutane Huɗu Da Ake Zargi Da Hannu Cikin Kashe Shugaban Кasar

'Yan sanda a ƙasar Haiti sun bindige wasu mutane huɗu da suke zargi da hannu a kisan gillar da aka yi wa shugaban ƙasar Jovenel Moïse da kuma kama wasu biyu na daban a wani musayar wuta da ta gudana a tsakaninsu.

ABNA24 : Shugaban ‘yan sandan ƙasar Leon Charles ne ya sanar da hakan wa manema labarai inda ya bayyana mutane huɗun da ‘yan sandan suka kashe a matsayin ‘sojojin haya’ yana mai cewa ‘yan sandan sun sami nasarar hallaka mutanen ne, waɗanda suka kashe shugaban a tsakar dare a gidansa, bayan wani gumurzu da musayen wuta da ya gudana tsakanin ɓangarori biyun.

A daren Laraban nan ne aka yi wa shugaba Jovenel Moïse ɗn shekaru 53 a duniya kisan gilla a gidansa da ke wajen birnin Port-au-Prince, bababn birnin ƙasar Haitin bayan harin da maharan suka kai masa inda kuma aka raunata matarsa, Martine Moïse, a harin da aka kai musu. Wasu rahotanni sun ce tuni aka kai ta birnin Florida don yi mata magani sakamakon mummunan raunin da ta samu.

Wasu bayanai sun ce maharan sun bayyana kansu ne a matsayin jami’an hukuma faɗa da muggan magunguna na Amurka kafin suka sami damar shiga gidan shugaban ƙasar inda suka aikata wannan aika-aika na kisan gillan.

Кasashe da kuma cibiyoyi daban-daban na duniya suna ci gaba da Allah wadai da wannan ɗanyen aikin da aka yi.

342/