Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Litinin

5 Yuli 2021

13:20:56
1157137

​Zanga-Zangar Adawa Da Shugaban Brazil Na Kara Bazuwa A Fadin Kasar

Al’ummomin kasar Brazil a birane daban-daban na kasar na ci gaba da yin kira ga shugaban kasar da ya gaggauta sauka, sakamakon zarginsa da ayyukan cin hanci da rashawa.

ABNA24 : Rahotanni daga kasar ta Brazil na cewa, dubun-dubatar mutanen kasar ne suke gudanar da zanga-zanga da gangami a biranan kasar, domin yin tofin Allah tsine da salon mulkin shugaban kasar Jair Bolsonaro, wanda ake zarginsa da ayyukan cin hanci da rashawa a bangaren sayen allurar rigakafin corona, da kuma kasa tabuka komai wajen magance wannan matsala, wadda ta yi sanadiyyar salwantar rayukan dubban daruruwan mutanen kasar.

Tun bayan barkewar cutar corona da kuma yadda ta yi tasiri a kasar Brazil, al’ummomin kasar da dama suke nuna rashin gamsuwarsu da salon mulkin Bolsonaro wanda babban abokin tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ne, yayin da kuma a halin yanzu lamarin yake daukar sabon salo, inda ake yin kira a gare shi da ya sauka daga kan karagar shugabancin kasar.

Da dama daga cikin mutanen kasar Brazil dai suna karkata ga shugabancin tsohon shugaban kasar ta Brazil Lula Inacio da Silva, wanda ake ganin ga dukkanin alamu zai iya sake dawowa kan shugabancin kasar, matukar dai ya sake tsayawa takara.

342/