Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Jummaʼa

2 Yuli 2021

18:21:02
1156109

Sojojin Amurka Sun Bar Babban Sansaninsu A Afghanistan Bayan Shekaru 20

Shekaru ashirin bayan mamayar da suka yi wa ƙasar Afghanistan, a yau sojojin mamayan da Amurka take wa jagoranci sun fice daga babban sansanin sojojinsu a ƙasar ta Afghanistan da ke garin Bagram, kimanin mil 45 arewacin birnin Kabul, babban birnin ƙasar Afghanistan ɗin.

ABNA24 : Rahotanni daga ƙasar Afghanistan ɗin sun bayyana cewar a yau Juma’a ce sojojin Amurka suka miƙa wa dakarun Afghanistan ɗin sansanin sojin na Bagram, wanda ya kasance babban wajen da sojojin Amurka suke ƙaddamar da hare-harensu, a hukumance.

Sansanin na Bagram wanda ya ke da manyan hanyoyin saukar jiragen sama bugu da ƙari kan manyan gine-gine ya kasance wajen da dubun dubatan sojojin mamaya na ƙasashen waje suke shigowa ƙasar Afghanistan ɗin tsawon shekaru ashirin ɗin da suka gabata, kamar yadda kuma wajen ya sha fuskantar hare-hare daga dakarun Taliban da sauran mayaƙa da suke adawa da kasantuwar Amurka a ƙasar.

Miƙa wannan sansani ga sojojin Afghanistan ɗin dai na daga cikin shirye-shiryen da gwamnatin Amurkan take yi na ficewa daga Afghanistan ɗin, wanda ake sa ran za a kammala shi a tsakiyar wannan wata na Yuli ko kuma ƙarshensa, kafin wa’adin da shugaban Amurkan Joe Biden ya ɗiba na 11 ga watan Satumba.

342/