Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Alhamis

1 Yuli 2021

11:55:18
1155824

Kwamitin Tsaro Ya Goyi Bayan Taron Vienna, Ya Buƙaci Amurka Ta Cire Wa Iran Takunkumi

Kwamitin Tsaron Majalisar Ɗinkin Duniya ya bayyanar da goyon bayansa kan taron Vienna da ake tsakanin Iran da wasu manyan ƙasashen duniya da nufin farfaɗo da yarjejeniyar nukiliyan Iran a aka cimma a 2015, kamar yadda kuma ya buƙaci Amurka da ta janye wa Iran takunkumin da ta sanya mata.

ABNA24 : Kwamitin tsaron ya bayyana hakan ne yayin zaman da ya gudanar don tattauna rahoton da babban sakataren MDD Antonio Guterres ya gabatar masa kan batun aiwatar da ƙudurin kwamitin mai lamba 2231 da ya amince da yarjejeniyar nukiliya.

Taron na jiya dai shi ne irinsa na farko da Kwamitin Tsaron na MDD ya gudanar tare da halartar jakadojin ƙasashe membobin Kwamitin tun bayan ɓullar annobar nan ta Korona.

A cikin rahoton da ya gabatar wa Kwamitin Tsaron, babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya buƙaci Amurka da ta cire dukkanin takunkumin da ta sanya wa Iran kamar yadda aka cimma hakan cikin yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma da ƙasar a shekara ta 2015, kamar yadda kuma ya buƙaci Iran ita ma a nata ɓangare da ta dawo cikin yarjeniyar da kuma girmama ta hanyar aiwatar da nauyin da ke wuyanta, wanda ta dakatar sakamakon rashin girmama yarjejeniyar da sauran ɓangarorin da aka cimma ta da su suke yi.

Buƙatar babban sakataren MDD tana zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa tsakanin ɓangarori daban-daban na yarjejeniyar na nufin sake farfaɗo da ita da kuma share fagen dawowar Amurka cikin yarjejenyar bayan da tsohon shugaban Amurkan Donald Trump ya fitar da ita a shekara ta 2018.

A nata ɓangaren Iran dai ta ce a shirye take ta sake dawowa cikin yarjejeniyar sosai da kuma girmama abin da aka cimma da ita matuƙar ɗaya ɓangaren yarjejeniyar shi ma ya girmama ta da kuma ɗage mata takunkumin da aka sanya mata kamar yadda aka cimma a baya.

342/