Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Alhamis

1 Yuli 2021

11:51:17
1155819

​Guterres Ya Bukaci Biden Da Ya Janye Takunkuman Da Amurka Ta Kakaba Wa Iran

Babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya bukaci shugaban kasar Amurka Joe Biden da ya janye takunkuman da Amurka ta kakaba wa kasar Iran.

ABNA24 : A cikin wani rahoto na kwamitin tsaron majalisar dinkin dinkin duniya, babban sakataren majalisar Antonio Guterres, ya kirayi shugaban kasar Amurka Joe Biden, da ya janye takunkuman da Amurka ta kaba wa Iran da suka shafi batun shirinta na nukiliya.

Antonio Guterres ya ce, yana kiran Joe Biden da ya dauki matakin kawo karshen takunkuman da suka shafi harkokin kasuwanci da kuam batun sayar da mai a kan Iran cikin gagagwa.

Wannan dai ya zo a daidai lokacin da mambobin kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya suke shirin gudanar da zama, domin yin dubi kan rahoton babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres, dangane da yadda aka yi aiki da yarjejeniyar nukiliya da aka kulla tare da Iran a shekara ta 2015.

A halin yanzu haka dai ana tattaunawa kan yadda za a farfado da wanann ayrjejeniya, amma Amurka tana ci gaba da jan kafa kan batun, inda taki amincewa ta janye dukkanin takunkuman da tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya dora wa kasar ta Iran a lokacin mulkinsa, wadanda sun sabawa doka da kuma yarjejeniyar da aka kulla, wadda Amurka tana daga cikin wadada suka rattaba hannu a kanta.

342/