Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Talata

29 Yuni 2021

11:13:02
1155097

​Hukumar Bada Agaji Ta Majalisar Dinkin Duniya Tana Shirin Rufe Ayyukanta A Duk Fadin Duniya

Hukumar bada agaji ta MDD ta bada sanarwan cewa ta na shirin rufe dukkan ayyukanta a cibiyoyi 12 da take da su a duniya, mafi yawansu a nahiyar Afirka da kuma Asia idan har kasashen duniya 193 suka kasa samar da kudaden da hukumar za ta yi amfani da su a shekara ta 2022.

ABNA24 : Shugaban hukumar Catherine Pollard ta bayyana cewa hukumar ta na bukatar dalar Amurka biliyon $6 don ci gaba da ayyukanta a dukkan cibiyoyinta 12 a duniya, amma idan har kasashen duniya sun kasa samar da wadannan kudade zuwa ranar Akhamis mai zuwa wato 30 ga watan Yuni, mai yuwa ta dakatar da ayyuykanta.

Pollard ta kara da cewa, sai dai MDD za ta dauki nauyin kula da kayakin hukumar a wadannan cibiyo 12 da take da su a duniya da kuma ma'aik’tanta.

Labarin ya kammala da cewa an sami tangarka tsakanin kasar Sin ko Cana da wasu kasashen turai kan samar da wadannan kudade.

Pollard ta kammala da cewa MDD ce take daukar nauyin kashi 28% na ayyukan hukumar, sai kuma kasar Cana wacce take daukar nauyin kashi 15% daga nan sai kasar Japan mai daukar nauyin kashi 8.5%.

342/