Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Talata

29 Yuni 2021

10:55:21
1155093

An Kai Hari Kan Sojojin Amurka A Siriya Bayan Umurnin Biden Na Kai Hari Kan ‘Yan Gwagwarmayar Iraƙi

Rundunar sojin Amurka ta bayyana cewar an harba wasu rokoki kan wani sansanin sojin Amurkan da ke ƙasar Siriya ƙasa da sa’oi 24 bayan wani hari da sojojin Amurka bisa umurnin shugaban ƙasar Joe Biden suka kai wasu sansanonin ‘yan gwagwarmayar Iraƙi a kan iyakar Iraƙi da Siriyan a jiya.

ABNA24 : Tun da fari dai kamfanin dillancin labaran Reuters ya ba da labarin cewa an kai hari da rokokin kan sansanin sojojin Amurkan ne a lardin Dayr al-Zawr a kusa da wata rijiyar mai da ke ƙarƙashin dakarun sa kai na SDF da suk samun goyon bayan Amurkan.

Yayin da yake magana kan harin, kakakin sojojin Amurka a yankin Coly Wayne Morrotto ya ce an kai hari wa sojojin Amurkan ne da yammacin jiya Litinin sai dai yace babu wani da ya rasa ransa sai dai ana ci gaba da gudanar da bincike don tantance irin hasarar da aka yi.

A jiyan ne dai sojojin Amurkan suka kai hari kan wani sansanin dakarun sa kai ‘yan gwagwarmayar Iraƙin da ke kan iyakan ƙasar da Siriya lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar huɗu daga cikin dakarun gwagwarmayar. Ma’aikatar tsaron Amurkan Pentagon ta ce an kai harin ne kan wasu wajaje da ake amfani da su wajen kai wa sojojin Amurkan hari kuma shugaba Biden ne ya ba da umurnin kai harin.

Dakarun gwagwarmayar dai na Hashd al-Sha’abi sun sha alwashin mai da martani kan wannan harin a kan sojojin Amurkan.

342/