Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Litinin

28 Yuni 2021

13:36:20
1154786

Amurka : Har Yanzu Ba A Ga Mutum 150 Bayan Ruftawar Gini A Miami

A Amurka har yanzu babu labarin mutum sama da 150 bayan da wani gini mai hawa 12 ya rusta a ranar Alhamis.

ABNA24 : Rahotanni daga AMurkar na cewa adadin mutanen da suka mutu sakamakon ruftawar ginin ya kai mutum tara a wannan Lahadin.

Masu aikin ceto na ci gaba da binciken ko za a samu ceto mutane daga cikin baraguzan ginin da ya rufta a arewacin Miami.

Da yawan iyalai sun kasa samun sukuni saboda rashin samun labarin 'yan uwansu.

Har yanzu dai ba a san dalilin da ya janyo rugujewar ginin ba mai shekaru 40.

342/