Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : parstoday
Lahadi

27 Yuni 2021

13:45:08
1154358

​Amurka: Ana Ci Gaba Da Neman Mutane Karkashin Ginin Da Ya Ruse A Florida

Mutane 4 ne aka tabbatar sun `mutu a kana 159 suka bace ya zuwa yanzu, biyo bayan rushewar wani gini na kusa da teku a kusa da gabar ruwan Miami, a yayin da masu aikin ceto ke ta kokarin lalube a baraguzan ginin, ko za su yi katarin zakulo wadanda ke da sauran shan ruwa.

ABNA24 : Magajiyar garin birnin, Daniella Levine Cava ta ce har yanzu hukumomi ba su kai ga samun labarin mutane 159 ba, wanda mai yiwuwa hakan yasa a kara samun adadin waeanda suka rasa rayukansu sakamakon aukuwar lamarin.

A yayin da al’ummar yankin ke cikin yanayi na tashin hankali, gwamnan jihar Florida ya bukaci cikakken bayani a game da ummul’aba’sin wannan al’amari na rugujewar bene mai hawa 12.

Tuni shugaban kasar Amurka Joe Biden ya bayar da umarni ga hukumomin kwana-kwana na jihar Florida da su kara zage dantse domin ganin an ceto wadanda suka da sauran kwana da suka lakahe a karkashin baraguzai.

Levine Cava ta ce, tun a shekarar da ta gabata masana kan harkokin gine-gine sun ce wannan ginin yana da matsala, musamman ganin yadda ya tsufa, da kuma yadda aka dora harsashinsa suna shakku kan ya zauna kan kasa yadda ya kamata.

An gina wurin ne dai tun sheakara ta 1980, wato shekaru 40 da suka gabata, wanda bisa tsarin gine-gine a kasar Amurka, gini mai shekaru haka yana bukatar a rusa shi ko kuma a yi masa wasu gyare-gyare da za su ba shi damar ci gaba da wanzuwa.

Har yanzu dai masu gudanar da ayyukan agajin gaggawa suna ci gaba da aikinsu ba hutawa, inda ake yin amfani da na’urori na musamman domin gano motsin mutane ko jin sautukansu, kamar yadda kuma ake yin amfani da karnuka wadanda aka bai wa horo domin gano mutane da suke karkashin barguzai.

Wannan dai na daga cikin irin hadararruka mafi muni da aka samu a kasar Amurka a cikin lokutan baya-bayan nan, wanda ya daga hankalin mutanen kasar matuka.

342/