Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Lahadi

27 Yuni 2021

13:39:32
1154352

An Ɗaure Ɗan Sandan Da Ya Kashe Floyd Shekaru Sama Da 22 A Gidan Maza

An yanke wa tsohon jami'in ɗan sandan Amurka farar fata Derek Chauvin hukuncin zaman gidan yari tsawon shekara 22 da rabi a kurkuku saboda samunsa da aka yi da laifin kisan gillan da aka yi wa baƙin fatan nan George Floyd a garin Minneapolis na ƙasar Amurkan.

ABNA24 : Yayin da ya ke yanke hukunci kan shari’ar, alƙalin kotun ya ce an yanke wa Derek Chauvin hukuncin ne saboda yadda ya yi amfani da matsayinsa na ɗan sanda ta hanyar da bata dace ba haka nan kuma da irin ƙetar da ya nuna ga Mista Floyd. Tun da fari dai kotun ta samu Chauvin, mai shekara 45 da laifin kisa da wasu tuhume-tuhumen da aka yi masa a watan da ya Mayun da ya gabata. Don haka alƙalin ya ɗag shari’ar sai zuwa jiya inda ya yanke masa hukuncin gidan zaman mazan. Yayin shariar dai lauyan Mr. Chauvin ya bayyana kisan a matsayin abin da ya kira "kuskuren da aka yi da kyakkyawar niyya". Iyalai da sauran magoya bayan Mr. Floyd dai sun yi na’am da hukunci duk kuwa da cewa suna ganin hukuncin da aka yanke masa ɗin yayi kaɗan. Mista Floyd mai shekara 48 ya mutu ne bayan da Chauvin ya danne masa wuya tsawon mintuna tara da rabi, lamarin da ya janyo mutuwarsa daga baya. Mutuwar Floyd ɗin dai ta janyo gagarumar zanga-zangar nuna adawa da wariyar launin fata da kuma cin zalin ‘yan sanda a Amurkan har ma da wasu ƙasashen.

342/