Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Litinin

21 Yuni 2021

13:34:43
1152544

Fitattu A Duniya, Sun Bukaci Biden Ya Tabbatar Da Kare Hakkin Falasdinawa

Fiye da kungiyoyi da fitatun mutane 680 a duniya, sun yi kira ga shugaban Amurka Joe Biden da ya mutunta alkawuran da ya dauka na kare hakkin dan Adam na Falasdinawa da kawo karshen mamaya da zaluncin Isra’ila akan Falasdinawan.

ABNA24 : A wata budaddiyar wasika da bangarorin daga kasashe 75 suka fitar, sun bukaci gwamnatin Biden da ta ba da tabbacin "za a tuhumi hukumomin Isra'ila da ke take hakkokin Falasdinawa".

Wasikar da bangarorin suka sanya wa hannu ta ce “Mu, kawancen shugabannin duniya da na kungiyoyin farar hula ’yan kasuwa, da jagororin addinai, siyasa da wadanda suka samu lambar yabo ta Nobel muna kira ga Amurka da ta dauki matakin da zai taimaka wajen kawo karshen mamayar da Isra'ila ke yi da cin zalin Falasdinawa da kare hakkokinsu na dan adam."

Sun kuma bukaci Biden da ta yi amfani da "matsin lamba na diflomasiyya" kan Isra'ila don kawo karshen "fadada wariyar launin fata da zalunci" da take yi wa Falasdinawa.

342/