Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Talata

15 Yuni 2021

14:52:34
1150786

​NATO:Batun Kasashen Cana Da Rasha Ne Suka Mamaye Taron Kungiyar Tsaro Ta Nato A Brussels

A taron da shuwagabannin kungiyar tsaro ta NATO kimani 30 suke gudanarwa a halin yanzu a birnin Brussels na kasar Belgium batun Cana da Rasha ne ya fi mamayar tattaunawar taron.

ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a gefen taron kuma shuwagabannin wadannan kasashen su na tattauna batun raya yarjejeniyar JCPOA ko kuma yarjejeniyar shirin nukliyar kasar Iran.

Kasashen Cana da Rasha dai su na ganin batun cewa sune abokan hamayyar kungiyar tsaro ta Nato ba gaskiya bane, don a cikin kungiyar akwai kawayen kasashen biyu, musamman kasashen Turkiyya da Jamus.

Labarin ya kara da cewa shuwagabannin kungiyar ta NATO su na wadannan maganganun ne kawai don ace kungiyar tana nan, amma akwai sabani mai tsanani a tsakaninsu.

342/