Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Litinin

14 Yuni 2021

09:34:32
1150466

Canada : An Yi Jana’izar Musulmin Da Aka Kashe A Harin Mota

A Canada daruruwan mutane ne suka halarci jana'izar iyalan nan Musulmai su guda hudu da wani mahari ya abkawa da mota a ranar Lahadin data gabata a birnin Landan na Canadar.

ABNA24 : An lullube gawar mamatan da turar kasar ta Canada, kafin daga bisani a yi masu jana’iza.

Harin dai ya bakanta rayukan mutane da dama, kuma Firaiministan kasar ta Canada, Justin Trudeau, ya danganta harin da na ta'addanci.

Kafin hakan dama ‘yan Sanda kasar, sun alakanta harin da na kiyaya, wanda aka kai ma mutanen kawai don suna musulmai.

A gobe Litini, ne ake gurfanar da matashin da ya bige mamatan da mota, wanda ake tuhuma da laifuka hudu na kisa.

342/