Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Asabar

12 Yuni 2021

10:30:05
1149801

Amurka Ta Gargadi Kasashen Cuba Da Venezuela Kan Sayan Makaman Iran

Wata magayar gwamnatin shugaban Biden na Amurka, wacce bata bayyana sunanta ba, ta fadawa jaridar Polotico kan cewa gwamnatin kasar tana jan kunnen kasashen Cuba da Venezuela kan karban makaman da suka saya daga kasar Iran.

ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wata majiya ta kasar Amurka ta na cewa Amurka zata daukar dukkan matakanda ta ga sun dace, don kare kawayenta a bangaren kudancin duniya.

Labarin ya kara da cewa jiragen ruwa dauke da makamai guda biyu ne a halin yanzu suke daba da isa kasashen don isar da makaman da kasashen biyu suka saya daga kasar Iran tun a zamanin tsohon shugaban Amurka Donal Trump.

Gwamnatin Amurka dai bata yarda da Nicolas Maduro a matsayin shugaban kasar Venezuela ba, kuma ta sha yunkurin kifar da gwamnatinsa amma ba tare da samun nasara ba. Kasar Cuba kuma tana karkashin takunkuman Amurka tunshekara 1959.

342/