Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Alhamis

10 Yuni 2021

10:30:24
1149279

Cibiyar Azhar Ta Mayar Da Kakkausan Martani Kan Kisan Musulmi A Canada

Cibiyar musulunci ta Azhar ta yi tir da Allawadai da kakkausar murya dangane da harin ta'addancin da aka kai wa musulmi a kasar Canada.

ABNA24 : Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya nakalto rahoto daga shafin Ahram Online cewa, babban malamin cibiyar musulunci ta Azhar a kasar Masar Sheikh Ahmad Tayyib, ya yi tir da Allawadai da kakakusar murya dangane da harin ta'addancin da aka kai wa musulmi a jihar Ontario ta kasar Canada.

Babban malamin an cibiyar Azahar ya ce, abin ya faru yana nuni da irin yadda masu tsananin kiyayya da musulmi suke kara karfia cikin kasashen turai, da kuma yadda ayyukansu na ta'addanci kan musulmi ke karuwa.

Ya ce irin wadannan mutane masu tsananin ra'ayin kin jinin musulmi da su da 'yan ta'addan Daesh duk abu guda ne, 'yan ta'adda ne makasa bil adama, kuma dukkaninsu suna kashe musulmi ne ba tare da wani banbanci ba.

A kan haka ya ce lokaci da gwamnatocin kasashen duniya musamman na kasashen turai, za su mike su kamar suna yi wajen fuskantar wannan barazana mai matukar hadari ga makomar kasashensu.

Shi ma a nasa bangaren babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya yi Allawadai da kakkausar murya kan kisan musulmi da aka yi a kasar Canada, tare bayyana hakan a matsayin aiki na dabbanci da ta'addanci.

342/