Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Litinin

7 Yuni 2021

12:00:10
1148348

Guteres, Ya Ji Takaicin Labarin Kisan Fararen Hula 138 A Burkina Faso

Babban sakataren majalisar dinkin Duniya, Antonio Guterres ya ce ya ji takaci da jin labarin kisan fararen hula 138 a kauyen Silhan na Burkina Faso a cikin daren Juma’ar data gabata.

ABNA24 : Hare haren na baya bayan nan su ne mafi muni a kasar, tun bayan soma rikici mai nasaba da gungun kungiyoyi masu ikirari da sunan jihadi a shekarar 2015.

A wata sanarwa da ta samu sa hannun kakakinsa, Stephane Dujarric, Guterres ya bayyana bacin ransa a game da kashe kashen daruruwan farar hula da suka hada da mata da yara.

Guterres ya caccaki wannan ta’asa, sannan ya jaddada bukatar kasashen duniya su rubanya goyon bayan da suke bai wa kasashen da ke fama da matsalar ta’addanci.

Babu dai wata kungiya da ta yi ikirarin kai harin.

342/