Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Lahadi

6 Yuni 2021

13:41:24
1148010

​MDD : Farashin Abinci A Duniya Ya Yi Tashin Da Ba'a Bata Gani Ba Cikin Shekaru 10

MDD : farashin abinci a duniya ya tashi cikin sauri a wata guda fiye da kowane wata a shekara 10

ABNA24 : MDD ta yi amfani da alkaluman hauhawar farashi na duniya, wanda ya yi tashin gwauron zabi sama da wata 12 a jere.

Shirin samar da abinci na MDD ya bibiyi alkaluman farashin abinci a fadin duniya, wadanda suka hada da nama, sikari da abincin da aka sarrafa daga hatsi da mai da dai sauransu.

A wannan shekara farashin na karuwa da 39.7 a watan Mayu, tashin farashin wata guda da ba a bata gani ba tun watan Oktoba 2010, kamar yadda alkaluman suka bayyana.

Wannan ya haifar da tashin farashin kayan wanda tun Satumbar 2011 rabon da a ga haka.

342/