Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Lahadi

6 Yuni 2021

13:37:36
1148007

Amurka Da Iraki Sun Cimma Yarjejeniya Ta Fidda Sojojin Kasashen Waje Daga Kasar

Mataimakin shugaban kwamatin hadin guiwa na sojojin kasashen Amurka da Iraki, ya bayyana cewa kasashen biyu, sun cimma matsaya ta fidda sojojin Amurka daga kasar Iraki.

ABNA24 : Jaridar Assabah ta kasar Iraki ta nakalto Abdul-Amir Asshamari, ya na fadar haka bayan kammala taron kwamitin hadin guiwa na sojojin kasashen biyu a jiya Asabar a birnin Bagdaza babban birnin kasar ta Iraki.

Asshamiri ya kara da cewa kasar Iraki a halin yanzu ba ta bukatar samuwar sojojin Amurka a cikin kasar. Sannan aikin hadin guiwar da kasashen biyu za su yi a fafatawa da mayakan kungiyar Daesh za su takaita ne ta musayar bayanai da kuma ayyukan leken asiri.

Tun farkon shekara ta 2020 ne majalisar dokokin kasar Iraki ta bukaci sojojin kasashen waje gaba daya su fice daga kasar.

342/