Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Jummaʼa

4 Yuni 2021

15:57:28
1147538

Habasha Ta Sake Watsi Da Takunkuman Amurka

Kasar Habasha, ta sake watsi da takunkuman Amurka, tana mai dangantan takunkuman da shishigi a harkokin cikin gidan ta.

ABNA24 : Amurka ta kakawa mahukuntan Adis Ababa takunkumi ne kan abunda ta kira da take hakkin dan adam a yankin Tigrey.

Saidai a daidai lokacin da al’amuran a yankin na Tigray ke kara tabarbarwa gwamnatin Habashar na mai cewa ita ce yaunin daidaita al’amura a yankin ya rataya a wuyanta.

A halin yanzu dai takkadama na kara kamari tsakanin Amurka da kuma kasar ta Habasha.

Amurka dai ta kakaba wa gwamnatin Habasha takunkumi ne yau da wattani bakwai da suka gabata bayan barkewar rikici a yankin na Tigray.

Habasha dai ta ki amince sanya hannu duk wasu kasashen waje a rikicin yankin, inda ta ce abunda take bukata shi ne kawai a taimaka ma ta da yadda zata tunkari lamarin, a cewar kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Dina Mufti.

Wasu alkalumma da shirin samar da abinci na MDD, ya fitar sun nuna cewa mutane miliyan 5,2 ne kwatankwacin kashi 91% na al’ummar Tigray ne ke bukatar tallafin abinci na gaggawa.

342/