Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Litinin

31 Mayu 2021

12:57:25
1146219

An Yi Zanga zangar Kyamar Amurka Kan Sanyawa Habasha Takunkumi

A kasar Habasha, gomman mutane suka gudanar da wata zanga zanga a Adis Ababa babban birnin kasar domin yin tir da takunkuman baya baya nan da Amurka ta kakaba wa kasar.

ABNA24 : Masu zanga zangar da suka fito bisa kiran gwamnati, na masu nuna bacin ransu kan takunkuman da Amurka ta sanya wa kasar game da rikicin yankin Tigray.

Amurka dai na mai zargin mahukuntan kasar ta Habasha da toye hakkin dana adam a yankin na Tigray mai fama da rikici, lamarin da ‘yan Habashan ke dangantawa da shishigi a harkokin cikin gidan kasar.

Takunkuman na Amurka dai sun shafi mahukuntan Habasha da Erytrea kan rawar da suka taka a rikicin yankin Tigray, saidai mahukunatn kasashen sun ce takunkuman haramtatu ne.

342/