Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Litinin

31 Mayu 2021

12:53:51
1146214

Wakilin MDD Kan Rikicin Yemen Ya Gana Da Abdul Malik Hutshi

Wakilin MDD na musamman kan rikicin kasar Yemen Martin Griffiths ya gana da Sayyid Abdul Malik Huthi shugaban gwamnatin tsamar da kasa ta kasar Yemen a safiyar yau Lahadi.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Fars na kasar Iran ya bayyana cewa Sayyid Abdul Malik a ganawarsa da Griffiths ya bayyana rashin amincewarsa da yadda MDD ta hada al-amuran da suka shafi jinkai da kuma ayyukan soje da siyasa.

Har’ila yau Griffiths ya gana da wasu jami’an gwamnatin kasar ta Yemen dangane da tsagaita budewa juna wuta da kuma ayyukan bada agajin gaggawa ga mutanen kasar wadanada suke fama da karancin abinci.

Kafin haka a makon da ya gabata ne Griffiths ya je kasar Saudia inda ya gana da shuwagabannin kasar dangane da wannan batun.

342/