ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyanan cewa dokar wacce sanata James Lankford, John Cornyn da kuma Tim Scott suka gabatar ta sami goyon bayan tsohon sakataren harkokin wajen kasar ta Amurla Mike Pompeo.
Dokar ta bukaci a ci gaba da dorawa kasar Iran takunkunman tattalin arziki mafi tsanani, har sai da dawo kan yarjejeniyar JCPOA sannan ta daina abinda suka kira shihsigi a cikin al-amuran kasashen kudancin Asia sannan da takatar da shirinta na makamai masu linzami.
Wadannan sanatoci dai sun kaddamar da wannan bukatarne a dai-dai lokacinda ake tattaunawa tsakanin kasshen da suka rage a yarjejeniyar ta JCPOA suke son dawo da Amurka cikinta.
Tuni dai gwamnatin shugaba Biden ta amince ta dage manya manyan takunkuman tattalin arzikin da aka dorawa kasar, wadanda suka hada da sayar da danyen man fetur da kuma Bankuna, amma Iran ta na bukatar fiye da haka nesa ba kusa ba.
342/